Mukaman Sarauta a Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙaman Sarauta a Kano


Galadima: An fara naɗa sarautar galadiman Kano a zamanin Sarkin Kano Warisi (455 – 488). Daga baya, bayan zuwan Fulani sai aka gadar da ita a gidan Fulani Sulluɓawa.
Madaki: Sarkin Kano Warisi ne ya fara naɗa sarautar Madawaki. Yana daga cikin ‘yan majalisar zaɓen sarkin Kano a yanzu.
Makama: Sarkin Kano Warisi ne ya fara naɗa makaman Kano. A yanzu duk wanda ke riƙe da wannan sarauta yana daga cikin manyan ‘yan majalisar sarki sannan kuma ɗan majalisar zaɓen sarkin Kano kuma hakimin Wudil.
Sarkin Dawakin Tsakar Gida: An fara yin wannan sarauta a lokacin Sarkin Kano na 29, Muhammadu Lawan Kutumbi.
Ɗan Iyan Kano: Sarautar ɗan iyan Kano sarauta ce ta ƙanin sarki wanda suke ɗaki ɗaya; wato mahafiya da mahafi duk ɗaya ne da sarki. Abin da ake kira shaƙiƙi a shari’ance. Zamanin Sarkin Kano na 23, Muhammadu Kisoke ko Kisakewa aka fara yin wannan sarauta.

Sarki yana da wani ƙani wanda mahaifiyarsu take matuƙar ji da wannan ɗa nata. Saboda haka ta saka sarki ya yi masa wannan sarauta.
Limamin Kano: An fara naɗa babban limamin Kano a zamanin sarkin Kano na 11, Ali Yaji. A zamanin da su Sheikh Abdurrahman Zaite suka zo Kano da karatun addinin. Kasantuwar sarki ya karɓi wannan addini kuma addini ya zama na gwamnati, sannan kuma an gina makarantu da masallatai a duk faɗin masarautar Kano, sai aka naɗa limamin Kano.

Sarautar Bayi

  1. Shamaki: Wannan ita ce sarauta mafi girma a sarautar bayi a Kano.
  2. Ɗan Rimi: Ita ce sarauta ta biyu a daraja a sarautar bayi a Kano. Ba a tantance zamanin sarkin da aka fara yinta ba, amma tun kafin zuwan Fulani akwai wannan sarauta a Kano.

    Duk wai riƙe da wannan sarauta shi ke kula da harkokin da ke gudana tsakanin sarki da hakimai, harkokin iyalin sarki da suka haɗa da kula da abincinsu, harkar sutura, ɗaure-ɗauren aurensu da saursansu. Sannan kuma shi yake kula da gine-ginen sarki.

  3. Sallama: Sarkin Kano Kanajeji ne ya fara naɗa wannan muƙami na sallaman sarki. Shi kuwa sallama kamar muƙamin PA ne a yanzu. Ayyukansa a gidan sarki sun haɗa da bayar da izinin ganin sarki ga duk mai son ganin sarki a ciki da wajen gida sannan kuma a koda wane lokaci.

    Ibrahim Kanajeji ya samar da wannan sarauta ne domin samar da kafar da za ta bayar da damar sanin dukkanin mutumin da ya gana da sarki domin gudun afkuwar ta’asar da Usmanu Zauna Gawa ya aikata na kashe sarkin da ya gabace shi.

    Amintaccen sarki; wato wanda sarki ya aminta da shi sosai ake naɗawa a kan wannan kujera.

  4. Kasheka: Kasheka sarauta ce ta bayi. Babban aikin duk mai riƙe da wannan sarauta shi ne zama tare da sarki a kodawane lokaci kuma a kowane guri. Duk gurin da sarki zai je dare ko rana, Kasheka yana tare da shi.

    Ita ma wannan sarauta Sarki Kanajeji ne ya samar da ita saboda sake inganta tsaro ga rayuwar sarki.

  5. Kilishi: Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ne ya fara yin wannan sarauta. Shi kuwa Kilishi, bawan sarki ne wanda alhakin yi wa sarki shimfiɗa ya hau wuyansa. A duk gurin da sarki zai zauna, to kilishi ne yake yi masa shimfiɗa.
  6. Sarkin Hatsi: Shi ne mai kula da kayan abincin gidan sarki. Shi ne yake fitar da zakkar sarki, shi yake fitar da zakkar kono, shi yake rarraba ragunan sarki da sauran ayyukan da suka danganci wannan a lokacin da suka dace sannan kuma ya bayar da su ga waɗanda suka dace.
  7. Maja Siddi/Sirdi: Maja Siddi shi ne wanda yake kula da dawakan sarki da kuma raƙumansa. Shi yake kula da abincinsu, kayan adon dawakai, kayan siddinsu shi yake zaɓar dokin da sarki zai hau sannan ya shirya shi da sauran abubuwan da suka danganci dawakai.
  8. Sarkin Kakaki: Shi ne mai busa kakakin sarki. Shi kuwa wannan abin busa ana busa shi ne a duk lokacin da sarki zai fito; waton abin sanarwa ne, da shi ake sanar da jama’a cewa ga sarki nan zai fito. A zamanin sarkin Kano Muhammadu Rumfa aka fara naɗa wannan sarauta. Kasantuwar shi kansa abin busar a lokacin nasa aka fara busa shi.
  9. Sarkin Dogarai: Shi ne mai kula da ddukkan ayyukan dogarai. Ƙari a kan haka kuma shi yake ɗora sarki a kan doki.

    Su kuwa dogarai su ne jami’an da suke kula da lafiyar sarki, samar da tsaro a fadar sarki da gari baki ɗaya, kamo dukkan wanda ya aikata wani lafin da ya cancanci a gurfanar da shi a gaban sarki, da sauran ayyukan da suka shafi kula da kuma aiwatar da doka.

  10. Sarkin Figini: Shi ne mai yi wa sarki firfita da maficin gashin jimina. Sarautar da maficin duk a zamanin Muhammadu Rumfa aka fara yin su.
  11. Zagage: Suna ne na jama’u, kasantuwar ba mutum ɗaya ne yake aikin ba tun asali. Su kuwa zagage bayi ne da suke wucewa gaban sarki a lokacin da yake tafiya a ƙasa ko a kan doki ko raƙumi. Daga nan aka samo kalmar bita zaizai, zagin aikatau, da sauransu.

    Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo shi ya fara yin wannan sarauta. Sannan kuma duk wani mai riƙe da muƙamin sarauta tun daga kan ‘yan majalisa har zuwa hakimai to duk suna da zagage. Sai dai, sarki ne kaɗai yake da ikon naɗa zagage guda goma sha biyu rus. Ana zaɓo shida daga cikin ‘ya’yan sarki, shida kuma bayi.

  12. ‘Yan Lifidi: A zamanin Sarkin Kano Kanajeji aka fara wannan sarauta.
  13. ‘Yan Kwalkwali: A zamanin Sarkon Kano Kanajeji aka fara yin wannan sarauta.

Manazarta:


Al-Illori A. A. (1987). Al-Islami Fiy-Nijeriya wa Sheikh Usmanu Bn Fodiyo Al-Fullanniy Al-Mujahidul Islamiyl Akbar Bi-Garb Ifrƙiyya Wal-Jaddil A’ala Asshahiid Ahmad Ballo. Markazul Ta’alimul Arbiy Al-Islamiy, Agege-Nijeriya.

Boahen A. (1965). Topics in West African History. Printed in Malaysia.

Gumi A. M. (Babu Shekarar Bugu). Alƙur’ani Mai Girma da Kuma Tarjamar Ma’anoninsa Zuwa ga Harshen Hausa. Alƙur’ani da aka buga a Madina garin Manzo, wuri da aka tanada musamman na Sarki Fahad don buga Alƙur’ani Mai Girma. Madina.

Wazirin Kano A. A. (1978). Kano ta Dabo Cigari. Northern Nigerian Publishing Company Limited. Zaria, Kaduna-Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub